Rahotanni daga jihar Gombe sun tabbatar da cewa dan majalisar dokokin Gombe mai wakiltar Akko ta Yamma, Hon. Abdullahi Abubakar ya arce da sanda iko na majalisar dokokin a lokacin da ake yunkurin tsige Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Mohammed Haruna.
A ranar 5 ga watan Mayu ne dai, Shugaban Marasa Rinjayen ya kira taron manema Labarai inda ya nuna cewa an yi rashin adalci a zaben Shugabannin jam’iyyar APC na jihar, wanda a kan haka wasu suka nemi a tsige shi amma kuma ‘yan Majalisa hudu daga cikin su takwas na APC ba su goyi bayan hakan ba.