Wani Dan Majalisa Ya Gabatar Da Kudirin Hanna Matasa Yin Cacar Naija Bet


Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sokoto ta arewa ta daya a majalisar Hon Malami Bajare a ranar Laraba ya kai kokensa kan yadda matasa kashi 70 cikin 100 suka tsunduma a cikin cacar naija bet, wadda hakan ya sabawa koyarwa irin ta addinin islama, haka zaliki tarbiyar matasa da dama ta fara gurbacewa a ta dalilin haka.

Ya kara da cewa naija bet caca ce da ta samo asali shekaru dari da doriya wadda aka kirkira domin a hallakar da dubban musulmi, shi ya sa aka sako harkokin wasanni a cikinta domin an san musulmai da yawa suna sha’awar harkokin wasanni musamman kwallon kafa.

Daga karshe ya yi kira da a yi kokarin ganin cewa an dakile wannan wuta da ta taso mai kokarin kona dukkanin tarbiyar da aka san jihar Sokoto da ita, ta hanyar yakar shugabanni wannan lalura.

Muna rokon Allah ya taimaki Malami Bajare akan irin wadannan kudurorri masu amfani da yake kaiwa gaban majalisa.

You may also like