Wani dan majalisar wakilai ya sha ruwan duwatsu a mazabarsa


Wasu mutanen mazaba da suka fusata sun yi ruwan duwatsu akan dan majalisar wakilai, Garba Hamma Julde daga jihar Taraba.

Julde na wakiltar mazabar Bali/Gassol a majalisar wakilai ta tarayya.

Mutanen mazabar a ranar Asabar an rawaito sun jefa duwatsu akan dan majalisar bayan da suka zarge shi da yin watsi da su.Ya raba baburan hawa 11 ga shuwagabannin mazabu da kuma mota guda ga shugaban jam’iyar APC na karamar hukumar Bali.
Kafin jami’an tsaro su dauke shi ya zuwa matsira dan majalisar ya samu rauni sakamakon jifan.

Musa Sandirde, wani da ya sheda abin da yafaru ya ce an kai wa dan majalisar hari dai-dai lokacin da ya kammala jawabinsa kuma  yake shirin mika makullan ababen hawa ga shugabannin jam’iyar APC na karamar hukumar Bali.

Sandirde ya ce mutanen mazabar sun ci alwashin kin sake zabensa a shekarar 2019.

You may also like