
Wani yaro mai ƙarancin shekaru ya kashe mutane uku sakamakon tuƙin ganganci a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Gusau ranar Laraba, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Muhimmad Shehu ya ce rundunar tana nan tana binciken lamarin.
“Lamarin ya faru ne ranar Litinin kuma ya zuwa yanzu ba a gano yaron da ya buge mutanen ba, tuni muka samu cikakken bayaninsa a cigaba da binciken da muke yi,”ya ce.
Da yake magana akan batun mai maganar da yawun hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC a jihar, Nasiru Ahmad ya ce sun samu labarin faruwar lamarin.
“Mun samu labarin ne bayan da ƴan sanda suka ɗauke gawarwakin mutanen saboda haka maganar yanzu tana hannun ƴan sanda,” ya ce.
Wani shedar gani da ido yace direban ya sheƙo motar ƙirar Marcedez inda ta ƙwace kuma ya yi kan mutanen.
Daya daga cikin waɗanda suka mutu ɗaliba ce dake ajin ƙarshe a makarantar koyon aikin jinya da unguwar zoma dake jihar