WANI DIREBA YAYIWA YAR BAUTAR KASA FYADE DAGA BISANI YA KASHE TA 



Wani mai aiki da wata makarantar koyar da tukin Mota, Lizzu Driving School dake garin Abekuta na jihar Ogun mai suna Festus Udo ya hallaka wata budurwa ‘yar bautan kasa sakamakon fyade da ya yi mata. 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu ne ya bayyana haka a ranar Larabar da ta gabata, yayin da ya jagoranci ‘yan jaridu zuwa inda Udo ya yi wa budurwar mai suna Modupe Taiyesi fyade da karfin tuwo, daga bisani kuma ya kashe ta, inda aka tarar da gawar ta fara rubewa. 

Majiyarmu ta Premium Times ta ruwaito kwamishina Iliyasu yana fadin Udo ya yaudari Modupe ne da karyar zai koya mata tuki, sannan ya samar mata izinin tuki, don haka ne ta yi rajista da makarantar koyon tuki.

Shugaban hukumar bautan kasa ta jihar Ogun, John Okon ne ya shaidawa kwamishinan cewa wata daga cikin masu yi masa kasa hidima a jihar ta bace, daga nan ne ‘yan sanda suka fara bin diddigi.

 “Binciken mu ya kai mu ga wani mai suna Fetus Udoh, wanda ke koya ma Madupe tuki, da haka ne har muka kai ga kama shi, tare da gano inda ya bar gawar budurwar. Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, bayan Udo ya kira ta, tazo su yi tuki, shi ne ya kai ta har zuwa wannan daji.” Inji kwamishinan. 

Shi ma wanda ake tuhumar ya shaidawa ‘yan jaridu cewa “Bayan na kai ta zuwa dajin, sai na fada mata ina so in yi amfani da ita, amma ta ki, ni kuma sai na ja ta da karfin tuwo zuwa dajin nan, kuma na zakke mata, bayan na gama ne, sai ta ce sai ta fadawa ‘yan uwanta, ni kuma sai na yaga rigar ta, na shake mata wuya da shi.”

You may also like