Wani Fasto Ya Rataye Kansa Har Lahira  a Kaduna Rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa wani malamin addinin Kirista mai suna Fasto Samuel Hamza ya rataye kansa har lahira a gidansa dake Unguwan Rimi a cikin garin Kaduna.

An ruwaito cewa Faston ya rataye kansa ne da igiya wadda ya daure a jikin fankar da ke cikin dakinsa. Makwaftansa ne suka gano shi bayan da suka balle kofar dakin nasa bayan ba su ji doriyarsa ba kamar yadda suka saba. Tuni dai rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan al’amarin.

You may also like