Wani Fasto Ya Yiwa Matan Cocinsa 20 Ciki


Wani fasto dan shekara 53 da aka kama da laifin yi wa mata 20 mabiya cocinsa ciki ya yi ikirarin Ruhi Mai Tsarki ne ya umarce shi da yayi jima’i da su.

A yanzu dai rundunar ‘Yan sandan Nijeriya ta damke Timothy Ngwu sakamakon keta haddin yara mata da ma manyan a cocin “Vineyard Ministry of the Holy Trinity”.

Mummunar halayyar Ngwu ta dai zo karshe sakamakon rahoton da sakakkiyar matarsa Veronica ta kai wa ‘yan sanda. Veronica dai ta gaji da mummunar halayyar faston ta zinace-zinace, wacce har ta kai shi ga lalata da wata diyar ‘yar uwarta.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Enugu ya sanar wa jaridar Naij.com cewar faston ya yi ikirarin yin biyayya ga tursasawar ruhi na ya aikata abin da Ubangiji ya so, ‘ba tare da la’akari da matar tana da aure ko babu ba.’

Ebere Amaraizu ya kara da fadin: ‘Idan matar ta haihu, yaron zai yi zaman din-din-din tare da mahaifiyar tashi a gurin bautar.’

Faston ya kuma sanar wa gidan jaridar cewar ya haifi yara 13 tare da mata daban-daban guda biyar.

Ya kuma yi ikirarin cewar bai taba saduwa da kowacce matar aure ba har sai idan mazajensu sun amince wa bukatar Ruhi mai tsarki na a aikata hakan.

Wasu mata masu suna Calista Omeje da Assumpta Odo sun bar mazajensu domin su zauna da faston sakamakon biyayya ga umarni mai tsarki.

Wata uwar ‘ya’ya takwas mai suna Odo ta ce Ngwu ya yi mata ciki, sannan yai wa ‘yarta ma ciki.

Sannan kuma Calista – wacce take da ‘ya’ya 10 tare da mijinta – ta ce faston ya mata ciki amma jaririn ya mutu. Sannan kuma ta ce ta bawa faston wata ‘yarta.

Dan uwan faston – wanda bai yarda da a ambaci sunansa ba ya ce, ya ja kunnen shi Ngwu din da ma iyalansu a kan halayyar faston amma suka ki su saurare shi.

Dan uwan nasa ya yi ikirarin cewar kama dan uwan nasa ba komai ba ce face fushin Ubangiji da ya fada masa. ‘Fushin Ubangiji ya fada wa dan uwana. Sau tarin yawa muna rokon shi da ya dena aikata abin da yake amma ya ki.

‘Ya mamaye mana guri, yana ta haihuwar yara ba tsari. Yana cewa muna masa hassada saboda yana aikata abin da Ubangiji ya umarce shi da ya aikata.’

‘Ya kori matarsa ta aure wacce ta haifa masa yara uku, sannan ya fada lalata da matan aure da ‘yan mata. Dubi gidan nan yadda yake cike da yara maza da mata.

‘Gaba daya mutanen gurin nan sakarkaru ne, ta yaya mace za ta bar mijinta saboda wani mutum daban da sunan bautar Ubangiji, sannan kuma ta aikata fasikanci? Ba zan taba iya sa kaina a cikin wannan sha’anin ba.

‘Su je can su warware da ‘yan sanda, amma ni ina son a rufe cocin gaba daya,” yayan nasa ya karasa.

You may also like