Wani Goggon Biri Ya Biyo Wani Manomi Gida A Jihar Cross River


Wani mutum ya bada labarin yadda gaba dayan wani kauye a Kuros Riba suka samu kansu cikin kaduwa bayan da wani nau’in gwagwgwan biri mai suna (Chimpanzee) ya biyo wani manomi gida.

Jama’ar kauyen Bitiah Irruan Boko da ke Jihar Kuros Riba sun samu kansu cikin yanayin kaduwa bayan da wani biri ya biyo wani manomi gida daga daji. Wani mai amfani da kafar sada zumuntar Facebook, Osang Gabriel, wanda ya ga aukuwar lamarin da idonsa ya watsa hotunan abun.

Gabriel ya rubuta: “Abun mamaki baya karewa. Gwagwgwan biri ya biyo manomi daga daji zuwa gida a bitiah Irruan Boki, Jihar Kuros Riba.

You may also like