Wani Jami’in Hukumar Kwastam Ya Rataye Kansa


Wani jami’in hukumar kwastam, mai mukamin mataimakin sufuritanda ya kashe kansa ta hanyar rataya, a kauyen Lungu dake Gwarinfa a Abuja. 

Har yanzu dai ba a san dalilin da yasa ya rataye kansa ba. 

Mutumin mai suna Christian dan shekara 44, ya kulle kansa ne a cikin daki, kana daga bisani ya rataye kansa. 

Majiyar jaridar Daily Trust tace, mutumin wanda bashi da aure, na zaune tare da dan uwansa,kuma a kwanakin baya ne akai masa canjin wurin aiki zuwa Lagos.

Shugaban caji ofis din yan sanda na Gwarinfa, CSP Nuruddeen Sabo, yace dan uwan marigayin yana shagon aski lokacin da lamarin ya faru. 

Yace an tabbatar da mutuwar mutumin a babban asibitin Kubwa.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutumin na fama da matsananciyar  damuwa. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like