
Asalin hoton, BBC Sport
Wani jami’in tsaro a filin wasa na Lusail ya fado daga bene ya mutu a lokacin karawa tsakanin Argentina da Netherlands a daf da na kusa da na karshe.
Dan kasar Kenya, John Njau Kibue na cikin hayyacinsa a lokacin da lamarin ya faru daga baya jikin ya motsa, bayan kwana daya da ya yi a asibitin.
Masu shirya Gasar Kofin Duniya a Qatar sun sanar da cewar suna bincike kan musabbabin da ta kai jami’in ya fado ya mutu.
‘Yar uwar mutumin mai shekara 24 ta sanar da CNN cewar kawo yanzu ba a sanar da su wani bayani ba da ya shafi hadarin.
”Muna son a yi mana adalci. Muna son sanin hakikanin abin da ya faru da ta kai ya mutu. Ba su aike mana da hoton wurin da ya fado ba, ba wani jawabi da muka samu har yanzu.” in ji Ann Wanjiru.
Kibue shi ne bako na biyu da yake aiki a Qatar da ya mutu tun fara Gasar Kofin Duniya ranar 20 ga watan Nuwamba.
Wani dan kasar Philippines ne ya fara mutuwa a lokacin da yake gyare-gyaren sansanin Saudi Arabia, kamar yadda The Athletic ta bayar da rahoto.
Wani rahoton da jaridar Guardian ta wallafa ta ce ma’aikata baki 6,500 ne suka mutu a Qatar, tun bayan da aka bai wa kasar izinin karbar bakuncin Gasar Kofin Duniya a 2010.
Argentina ta kai wasan karshe a Gasar Kofin Duniya, bayan da ta ci Croatia 3-0 ranar Talata.
Ranar Laraba za a buga daya wasan daf da kashe tsakanin Faransa mai rike da kofin da kuma Morocco wadda ta je wannan matakin a karon farko a tarihi.
Ranar Lahadi za a buga wasan karshe daga nan a rufe Gasar Kofin Duniya, sai shekara hudu nan gaba.