Wani Janar Na Isra’ila Ya Gargadi Netanyahu Kan Shiga Yaki Da Kungiyar Hizbullah


 

Tsohon shugaban majalisar tsaron Haratacciyar kasar Isra’ila Gayura Iland, ya gargadi gwamnatin Netanyahu da kada ta yi gigin shiga wani sabon yaki da kungiyar Hizbullah.

Janar Iland ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada da shi ta tashar talabijin ta 10 mallakin haramtacciyar kasar Isra’il, inda ya ce a halin yanzu kungiyar Hizbullah tana makamai masu linzami kimanin dubu 130, daga cikinsu kuma akwai masu matukar hadari, wanda kuma a halin yanzu Isra’ila ba ta makaman kariya da za su iya tare wadannan makaman na Hizbullah, ya ce yana magana ne bisa dogaro da rahotannin da kungiyoyin leken asirin Isra’ila suka tabbatar.

Tun kafin wannan lokacin dai wasu manyan hafsoshin sojin Isra’ila sun ya kunnen Netanyu, kan ya guji duk wani yunkuri na sake bude sabon yaki da Hizbullah, domin kuwa hakan ba zai yi wa Isra’ila dadi ba, domin kuwa a cewarsu yakin Syria ya kara bai wa mayakn Hizbullah wata kwarewa ta musammana  fagen yaki, inda a yanzu suke yaki a sahu tare da sojojin kundunbala na Rasha da Iran a cikin Syria, kamar yadda kuam suka samu tarin makamai daga Rasha kuma suka samu kwarewa wajen sarrafa su.

You may also like