Wani Jirgin Rasha Ya Bata Bayan Tashinsa Daga Birnin Sochi Zuwa Syria


4bkc7b3161eb23jyhp_800c450

Rahotanni daga kasar Rasha na cewa wani jirgi mallakin ma’aikatar tsaron kasar ya bata a safiyar yau, bayan tashinsa daga birnin Sochi zuwa birnin Latakia na kasar Syria.

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, jirgin yana dauke da mutane 91, da suka hada da ‘yan jarida 9, da kuma sauran mutane da za su tafi Syria domin murnan bikin kirsimati.

Bayanin ya ce ana zaton jigin ya fadi ne a cikin tsaunukan da ke kudancin kasar Rasha, amma har yanzu ba a kai ga tabbatar da hakan ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like