Wani Jirgin Sama Ya Fado A Kasar IndonesiyaWani jirgin saman horo ya fado a Indonesiya, inda ya yi ajalin mutane 13.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya fado ne a garin Timika na kasar Indonesiya a yayin da ake horar da matuka.
A halin yanzu ba a sanar da musabbabin hatsarin ba wanda ya faru a yankin da ake yawan anfani da jirgi ba.
A gefe guda kuma an sanar da cewa an samu gawawwakin mutanen da ke cikin jirgin.
Cikin shekarar da ta gabata irin wannan hatsari ya faru a kasar inda ya yi sanadiyyar mutuwar soji fin 100.

You may also like