Wani Kare Ya Hallaka Dan Gidan Zababben Shugaban Gambiya 



A yayin da yake fafitikar ganin an rantsar da shi a matsayin Shugaban. Kasa, zababben Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow ya gamu da wani abin bakin ciki bayan wani kare ya ciji dansa mai shekaru bakwai da haihu, Habibou Barrow, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
Rahotanni daga Babban birnin kasar wato, Banjul sun nuna cewa marigayin yana daga cikin ‘ya’yan Uwargidan zababben Shugaban wanda ke da mata biyu.

A halin yanzu dai, Adama Barrow yana kasar Senegal inda yake jiran an rantsar da shi a ranar 19 ga wannan wata idan har Shugaba Mai Barin Gado, Yahya Jammeh ya amince ya mika masa mulki.

You may also like