A ƙalla mutane 40 aka tabbatar suna ɗauke da cutar kanjamau a jihar Uttar Pradesh dake arewacin ƙasar Indiya bayan da wani likita da bashi da izinin yin aiki ya yi amfani da sirinji ɗaya wajen kula da dukkanin mutanen da yake dubawa.
Labarin da ya bazu a ranar Talata watanni bayan da mutanen da suka haɗa da yara da kuma mata an gano suna ɗauke da cutar lokacin da wata ƙungiya ke gudanar da gangamin kula da lafiya a shekarar da ta gabata a garin Bargamau dake yankin Unnao.
“Idan da anyi gwaji sosai a aƙalla za a iya samun mutane 500,”a cewar Sunil Bargamau wani kansila a yankin.
“An faɗa cewa mutane anan suna zuwa wurin wani likitan bogi domin kula da su.yana amfani da sirinji ɗaya da wajen kula da dukkanin su.”