Wani magidanci ya kashe matarsa a jihar Enugu


Rundunar yan sandan jihar Enugu ta ce ta fara cikakken bincike kan yadda wani mutum ya daki matarsa har ta ce ga garinku nan

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bakin, SP Ebere Amaraizu, ta bayyana cewa matar mai suna, Nkechi Nnamani,dake da yaya hudu na cikin koshin lafiya a makon da ya gabata kafin mjin na ta ya doke ta da wani abu a ka da ya jawo ta fita daga hayyacinta.Hakan ya jawo aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na Parklane dake Enugu anan aka tabbatar da mutuwarta.

Amaraizu ta ce lamarin ya faru ne a shahararriyar unguwarnan da ake kira Afia ‘9’ dake karamar hukumar Enugu ta arewa.

Haka kuma yan sanda sun fara bincike  domin  lalubo dalilan da suka jawo kisan ya yin da gawar Nkechi ke cigaba da zama a dakin ajiye gawarwaki

You may also like