A lokacin da ake ta samun rahotanni marasa dadi na wasu matan aure da ke hallaka mazajensu har lahira, shi kuma wannan jajirtaccen namijin rayuwarsa kacokan ya rasa gurin kubutar da rayuwar matarsa daga shokin din lantarki.
Ibtila’in ya afkawa wani iyali a Bauchi ranar Asabar, yayin da magidancin, Salihu Yahaya, ya rasa ransa gurin kokarin kubutar da rayuwar matarsa.
Yayin da yake bayanin abin da ya faru ga Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa (NAN), Sani Ahmed, wanda ya gabatar da kansa a matsayin daya daga cikin yaran mamacin, ya ce lamarin ya auku da misalin 6:40 na yamma.
Sani yake cewa: “Daya daga cikin matan marigayin, Halima, tana kokarin rataya jikakkun kaya a kan wata waya da suke shanya a cikin gidan. Bata sani ba ashe wayar ta hadu da wayar da ake sawa a saman katanga domin samar da tsaro ga gida, kuma wayar tana jone da lantarki.
“Nan take wayar ta rike ta. Karfin shokin din dole ya sa tai kukan neman taimako. Jin kararta ya sa marigayin ya garzaya gurinta domin ya kubutar da ita, inda yayi amfani da hannunsa gurin fizge wayar daga jikinta.
“Cikin rashin sa’a, a lokacin da ya garzaya domin ya kubutar da ita, yana yin alwalar zuwa sallar Magariba, kuma hannayensa akwai ruwa a jiki.
“Ya samu nasarar kubutar da matar tashi amma shi sai wutar tayi jifa da shi kasa bayan ta ja shi sosai. Allah cikin ikonsa sai rai yayi halinsa lokacin da aka yi gaggawar kai shi asibiti.
Sani ya ce shi da wasu mutane sun kai matar asibiti domin a duba lafiyarta, inda ya ce yanzu tana gida cikin koshin lafiya.
Lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa ya ziyarci gidan mamacin da ke layin NYSC a Fadaman Mada, Bauchi, bai samu damar tattaunawa da matar da abin ya faru a kanta ba sakamakon yananyin jimami da take ciki tare da amsar ‘yan gaisuwa.
Marigayi Yahaya ya bar mata biyu da ‘ya’ya shida.
ALLAH YA JI KANSA DA RAHAMA