Wani Magidanci Ya Yiwa Matarsa Da Diyarsa Ciki A Legas 


Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wani Magidanci a jihar Legas bisa tuhumarsa da yi wa matarsa da kuma diyarsa ‘yar shekara 13 ciki a lokaci guda.

Rundunar ‘yan sandan ta ce mahaifiyar matar Magidancin ne mai suna, Mista Saka Akonda dan shekaru 36 da haihuwa, ta fara gano cewa jikarta na dauke da ciki na wata shida sannan daga baya ta fahinci Uwar yarinyar ma na dauke da ciki na wata shida kuma duk Surukinta ne ya yi masu. A halin yanzu dai, an maka magidancin kotu.

You may also like