Wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda A Edo Ya Kashe Kansa


Wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Christopher Osakue ya halaka kansa garin Sokponba da ke birnin Benin ta jihar Edo.

Rahotanni na nuna cewa Mista Christopher ya sanya karamar bindigarsa ta aiki ya bindige kansa ne sakamakon kasa hakura da ya yi da halin cutar mutuwar barin jiki da ya same shi

Wannan hali ya sanya shi a jiya ya tura matarsa da dansa don su karbo masa wani sako, inda ya yi amfani da wannan dama ta kasancewarsa shi kadai a gida ya danna kunamar bindigarsa a gefen kansa

Mista Christopher dai bai bar wata takarda ta wasici ba kamar yadda wadanda ke aikata irin wannan halaya ta kashe kansu ke yi

Kafin rasuwar mataimakin kwamishina Christopher Osakue shi ne ke kula da horas da ‘yan sanda da kuma tabbatar da ci gaban tawagar ‘yan sandan jihar ta Edo bayan an yi masa canjin wajen aiki daga jihar Ondo

You may also like