Wani matashi mai shekaru 29 dan kasar Liberiya mai suna Mike Khailelu Jabateh ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bashi damar neman auren ‘yar sa Zahara Buhari.
Matashin ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook inda ya ce dukkanin wadanda ke shakkar batun sa da ya yi na cewar zai nemi auren ‘yar shugaba Buhari za su sha mamaki don kuwa shugaba Buhari har ya gayyace shi ya bayyanawa ‘yar ta sa son kowa kin wanda ya rasa irin soyayyar da yake mata.
Dama dai tun a ranar Alhamis 29 ga watan Satumba ne matashin ya bayyana a shafin nasa na Facebook cewa yana da niyyar ya nemi auren Zahra Buharin.
Haka kuma ya sanya hoton sa tare da matarsa ‘yar kasar Guinea inda ya ce yana da niyyar ya sake ta domin ya auri ‘yar shugaban kasar, domin ya gaji da zama cikin bacin rai.
Sai dai mutane da yawa a shafin na Facebook na ganin cewa wannan matashi zautacce ne, yana da tabin hankali, yayin da wasu kuma ke ganin yana yunkurin janyo hankalin mutane gare sa ne kawai.