Wani Matashi Ya Bar Musulunci Ya Koma kiristanci


Wani abokin gwagwarmayar mu a kafafen yada labarai kenan mai suna General Baba Sabana Afcort Yola da ya yi ridda daga musulunci zuwa kiristanci.

Biyo bayan samun wannan labari na komawarsa kirista, ‘yan uwa abokan gwagwarmayar social media sun yi ta cece kuce, inda da dama suka karyata hakan, saidai bayan tuntubarsa ta waya da aka yi ya tabbatar da gaskiyar labarin. Sannan ya yi rubutu a shafinsa na Facebook inda yake kara jaddada cewar lallai ya bar musulunci ya koma kirista.

Hakika banji dadin jin wannan labari ba, muna rokon Allah ya ganar da shi gaskiya.

Allah kuma ya kara tsare mana imanin mu a duk halin da za mu tsinci kanmu.

You may also like