Wani Matashi Ya Cafke Wani Ɗan Daba Da Ya Kai Masa Farkaki Cikin Dare A KanoWani matashi da ba mu iya tantance sunansa ba, ya cafke wani ɗan Daba da ya yi ƙoƙarin halaka shi a ciki dare dauke da makamai.
Matashin yace ɗan dabar ya ɗauko ƴan uwansa ƴan daba cikin dare, ɗauke da makamai domin halaka shi, sai dai ba su yi nasarar yi masa komai ba amma ya gane ɗaya daga cikinsu. Kuma ya kai rahoto offishin Anti Daba na shiyyar Fagge. 
Bayan kwana ɗaya  da faruwar lamarin ne Allah ya haɗasu a titin IBB dake cikin birnin Kano, nan take ya damƙe ƙugunsa kuma ya nemi ɗaukin al’umma domin su taimaka masa ya a kai shi ofishin na anti Daba. 
Sai dai wani babban mutum ya raba rigimar kuma ya ɗauki alƙawarin miƙa ɗan dabar zuwa hannun hukuma. 
Lamarin ya farune a yau Juma’a a daidai titin IBB dake Kano daura da gidan mai na ABY.

You may also like