Wani matashi wanda yake zaune a kauyen Alhajeri a mazb6ar Mai Rakumi, ta Karamar hukumar Mallammadori, ya kashe mahaifinsa mai suna Amadu Babare har lahira, ta hanyar sassara shi da wuka.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin din da ta gabata, bayan hatsaniya ta kaure tsakanin mahaifin yaro da dan nasa, inda dan yake zargin mahaifin nasa ba ya ba shi abinci, kuma ba ya kaunarsa. Wannan dalili ne ya sa yaron ya yi amfani da wuka wajen kashe mahaifin nasa har lahira.
Rundunar ‘yan sanda ta karamar hukumar Mallammadori sun yi nasarar cafke matashin, kuma likitocin sun tabbatar da rasuwar mutumin. Yanzu haka ‘yan sanda suna kan bincike inda da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kotu.
Wani mutum wanda ya zanta da wakilinmu kuma ya bukaci in boye sunansa, ya ce dama ko a watanin shida da suka wuce sai da matashin ya illata kakarsa ita ma da wuka kan wata hatsaniya.