Wani Matashi Ya Kashe Yayansa Saboda Tawul Ɗin Goge Jiki


Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato ta tabbatar da kisan da wani matashi ya yi wa wansa a dalilin wata ‘yar gardama da ta kaure a tsakanin su a kan tawul din wanka.

Wannan lamari dai ya faru ne yau Laraba, a kauyen Gwash da ke yankin Laminga a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Nyam wanda shi ne karami ya soka wa dan uwansa wuka ne, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Tyopev Mathias Terna ya bayyana cewa Nyam John wanda ya yi kisan yana hannun su, kuma da zarar an kammala bincike za a tura shi kotu. Yayin da aka ajiye gawar Joshua John a babban asibitin koyarwa na Jami’ar Jos.

You may also like