Wani Matashi Ya Kera Mota Mai Amfani Da hasken Rana A Kano


Muktar Ado matashi ne da ya yi amfani da basirarsa wajen kera mota mai amfani da hasken rana, a kokarinsa na fito da wani sabon abu a cikin al’ummarsa.

Ya ce sai da ya shafe shekaru biyu yana hada kayayyakin da zai kera motar kafin Allah ya ba shi sa’ar hadawa.

Motar dai an hada ta da karfe, batir guda hudu mai 36 voltage sai solar panel wato farantin dauko hasken rana sai tayoyi da wasu sauran kayayyaki.

Ya ce ya yi amfani da basirarsa domin kuwa har da rediyo a jikin motar, inda ya ce yana da burin bunkasa fasahar tasa domin ya inganta abinda ya fara.

Muktar ya ce iya nisan zangon karatunsa dai a sakandire ya tsaya kuma yana da burin cigaba da karatu, inda ya ce a halin yanzu matsi na rayuwa ne ya dakatar da karatun nasa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like