Wani Matashi Ya Rataye Kansa Saboda An Hana Shi Auren Masoyiyarsa A Jigawa


Wani Matashi mai Suna Inuwa Muhammad mazaunin unguwar Tudun Guru mazabar ‘Yan Koli a karamar hukumar Hadejia dake jihar Jigawa ya rataye kansa saboda an hana shi auren budurwarsa.

Yanzu haka yana ci gaba da karbar magani a asibiti.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hakan ta faru a cikin garin Hadejia, ko da satin da ya gabata ma wani matashi mai suna Umar Muhammad ya rataye kansa saboda hana shi auren masoyiyarsa.

You may also like