Wani Matashi Ya Yi Tattaki Daga Lagos Zuwa Zaria don Masoyiyarsa


Wani matashi mai suna Jimi Agbaje dan asalin jihar Legas ya yi tattaki daga Legas zuwa Zaria don Masoyiyarsa, Sharon Donald Wacce diya ce ga daya daga cikin gwamnonin yankin Neja Delta kuma a halin yanzu tana Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban masu tsaro na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Kanar J.K Tukur ne ya karbi matashin a Zaria inda aka garzaya da shi asibiti don duba lafiyarsa sakamakon wasu raunuka da ya samu a yayin tattakin.
Da yake bayyana dalilin yin tattakin, Jimi Agbaje ya ce a shekarar 2010 ne suka hadu da budurwarsa inda suka fara soyayya amma daga baya ta juya masa baya wanda a kan haka ne ya yanke shawarar yin tattakin zuwa Zaria saboda a nan ne iyayen yarinya suka hadu suka yi soyayya kafin su yi aure.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like