Wani matashi ya yiwa yarinya yar shekara uku fyade a jihar Benue


Wani matashin dan shekara 13 da aka boye sunansa an zargeshi da laifin yiwa yarinya yar shekara uku fyade a yankin Wadata dake cikin garin Makurdi babban birnin jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa matashin ya hilaci yarinyar inda ya kaita cikin makarantar firamare mallakar gwamnati dake kusa da majami’ar Holy Ghost dake kan titin asibiti a cikin garin Makurdi inda ya aikata lalata da ita.

Matashin na tsaka da aikata ta’asar ne lokacin da wasu yan kwallo dake horo a filin makarantar suka ganshi inda suka damka shi ga jami’an tsaro.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, Moses Joel Yamu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace mutumin da ake zargi ana tsare dashi a hedikwatar rundunar kuma za a gurfanar dashi gaban kotu da zarar an kammala bincike.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like