Matasa ya kamata su gane shan kwaya illa ne, wani matashi ya sari wani dan uwansa a kwebin wuya a sakamakon shan kwaya a karamar hukumar Sumaila dake jihar Kano, a cikin wani kauye a Magami mai suna Sansani.
Bayan ya sare shi an kai shi babban asibiti na Sumaila. A yayin da kuma jami’an tsaro suka tafi neman wanda ya yi wannan ta’addanci, sai aka same shi ya yanka kansa.
Zuwa yanzu dai shi ma yana asibiti rai hanun Allah.