Wani Matashi Yayi Wanka Da Madara Domin  Murnar Lashe Kofin Zakarun Turai Da Real Madrid TayiWasu daga cikin Hausawa magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na alakanta sunan kungiyar da Madara,ta la’akari da yadda sunan na Madrid  yayi kama da sunan madara a hausance.

Hakan yasa wasu da yawa daga cikin al’ummar Hausawa magoya bayan kungiyar suke kiranta da sunan “Madara” ko kuma suce “Madarar Kwallon kafa “.

Wannan dalili ne yasa wani matashi yin wanka da Madara domin nuna murnarsa ga nasarar da kungiyar ta samu na lashe kofin zakarun nahiyar Turai a karo na sha biyu. 

Sai dai ya yawa daga cikin mutane na ganin yin haka a matsayin wuce gona da iri. 

A kwanakin baya ma sai da wani matashi yayi wanka cikin kwatami domin nuna murnarsa da nasarar da kungiyar Barcelona ta samu. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like