Wani Ministan Buhari Na Ƙulla Maƙarƙashiyar Tsige Saraki – Isa Misau


Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Isa Misau ya zargi ministocin Shugaba Buhari da jagorantar wata makarkashiya na tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.

A yau ne, dan majalisar ya gabatar da wannan zargin a zauren majalisar inda ya nuna cewa a lokacin da majalisar ta je hutun Kirismeti da sabuwar shekara, wasu mutane a karkashin jagorancin Ministan sun rika shirya yadda za a tsige Saraki a matsayin Shugaban majalisar sai dai Sanata Misau bai bayyana sunan Ministan ba.

You may also like