Wani Mutum ya Cakawa Matarsa wuka har sau 124 a indiya.


wp-1471429181664.jpg

vllkytshh6ou4ii5s-503540e3Mutumin mai suna Sanjay Nijhawan dan shekaru 46 ya cakawa matarsa mai suna Sonita wuka har sau 124 wanda hahan yai sanadiyyar rasa rayuwarta, ba wani ne ya jawo hakan face neman da Sonita tayi na cecewar mijin nata daya sake ta, a maimakon sakin sai ya aika ta kiyama.

Sanjay dai ma’aikacin banki ne a Baclays Bank dake garin England, ya sara aikinsa na banki bisa dalilan da ba wanda ya sani. sun shiga halin kunci da rashin kudi tun bayan rasa aikin nasa da yayi, inda Sonita taga bazata iya jurewa bata bukaci Sanjay daya saketa.

A tuhumar da akai masa a kotu, ya shaidawa kotu cewa baya cikin hankalinsa a lokacin daya aikata kisan, domin a cewar sa dama yana da ciwon hauka wanda ciwon nasa ne ya tashi har yasa ya kashe matar tasa sonita mai shekaru 36.

masu bincike sun tabbatar da cewa Sanjay ya dade yana bincike a fejin Bincike na Google don sanin hanyoyin da zai amfani dasu wajen kashe kansa da kuma fasa kokon kan mutum.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like