Wani mutum ya hallaka kansa bayan ya kashe iyalinsa su biyar


Ƴan sanda sun tabbatar da cewa wani mutum mai matsakaicin shekaru, Stephen Nnadiogo, ya kashe kansa ta hanyar shan guba bayan da ya kashe   ƴaƴansa da kuma ƴar uwar matarsa ta hanyar caka musu wuka a yankin Awada dake Onitsha ta jihar Anambra.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin baturen ƴan sanda na Awada, Martin Chijioke, ya ce rundunar ƴan sanda ta fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

“Binciken farko ya nuna cewa mutumin da ake zargi bayan ya aikata kisan kan ya sha guba inda ya mutu nan take,”Chijioke ya ce.

Shedun gani da ido sun fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a gidan mutumin da ake zargi mai namba ta 21 layin Ntueke, unguwar Awada Obosi a ƙaramar hukumar Idemili ta arewa dake jihar.

 Majiyar ta ƙara da cewa matar mutumin bata gida lokacin da lamarin yafaru ya yin da yar aikin gidan ta gudu lokacin da lamarin yake faruwa.

“Kukan da yar aikin take ne ya ankarar da mazauna yankin bamu taɓa ganin faruwar irin wanna faruwar lamarin ba,”shedar gani da idon ya ce.

You may also like