Wani mutum ya karɓi bulala 6 kan satar wayar hannu da kuma yin cacaWata kotu dake Karmo a Abuja ta bada umarnin yi wa wani matashi mai suna Idris Isa, bulala shida saboda samun sa da laifin satar wayar salula da kuma yin caca.

Isa wanda yake zaune a ƙauyen Zango dake Karmo ya amsa dukkanin laifuka biyu da ake tuhumarsa da su da suka haɗa da  addabar al’umma da kuma yawace-yawace inda ya roƙi kotu ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun, Alhaji Abubakar Sadiq, shine ya bada umarnin bayan da mutumin da ake zargi ya amsa laifinsa kuma ya roƙi kotun kan tayi hukunci da sassauci.

Ya ce kotun baza ta yi masa sassauci ba a duk lokacin da ya sake bayyana a gabanta.

Mai gabatar da ƙara Misis Florence Avhioboh,ta fadawa kotun cewa wani mutum mai suna Aliyu Sulaiman dake kasuwar Karmo shine ya shigar da ƙara a ofishin ƴan sanda ranar 27 ga watan Janairu.

Mai gabatar da ƙarar ta cigaba da cewa mai laifin  a wannan ranar tare da wasu mutane d da ake nema sun taru a wurin da jama’a ke taruwa “suna yin caca da zummar yaudarar mutane.”

Mai laifin ya karbi wayar hannu ƙirar Itel a hannun  me ƙara wacce darajarta ta kai ₦11,000.

Ta ce yayin bincike ya amince da laifin da ya aikata kuma an samu samu nasarar gano wayar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like