Wani Mutum Ya Shafe Watanni 8 Yana Aikata Lalata Da Yarsa


Wata kotu dake Ikejan Jihar Legas ta tuhumi wani mutum mai suna Folorunsho Oluwaseun, da laifin yiwa yarsa mai shekaru goma 17 Fyade. 

Kotun ta bada belin Mista Oluwaseun kan kudi naira 300,000 da kuma mutane biyu daza su tsaya masa.

Mutumin da yake zaune  Ofin dake Ikorodun jihar Legas ,yana fuskantar tuhumar laifin aikata fyade. 

Dan sanda mai gabatar da kara Clifford Ogu, ya fadawa kotu cewa mutumin da ake zargi ya aikata laifin ne tsakanin 8 ga watan Agustan 2016, zuwa 7 ga watan Afirilun 2017.

Mista Ogu yace mutumin da ake zargi sun rabu da matarsa, tun shekarar 2013 , inda ya karbi rikon yayansa,su uku da suka hada da yarinyar.

“Mutumin da ake zargi ya fara aikata lalata da yar tashi tun daga watan Agustan shekarar da ta gabata.

“yarinyar ta rubuta a jawabin da tayiwa yan sanda,cewa duk lokacin da taki yarda yayi lalata da ita to yana hanasu abinci ita da yan uwanta. 

“Yarinyar ta fadawa mahaifiyarta abinda yake faruwa  lokacin da ta kaiwa yayan nata ziyara.

“Mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi a ofishin yan sanda dake Ikejan. ”

Laifin ya saba da sashi na 259, na kundin manyan laifuka na jihar Legas.

Alkalin kotun Majistire Taiwo Akanni ya daga shariar zuwa 5 ga watan yuni.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like