Rahotanni daga majalisar tarayya sun nuna cewa wani sabon rahoto da ya fito daga jami’an tsaron farin kaya ( DSS) ya nuna cewa Ibrahim Magu ya cika dukkanin sharuddan zama cikakken Shugaban Hukumar EFCC.
Tun da farko dai, majalisar ta samu wani rahoto daga hukumar DSS ta hannun Shugaban Ma’aikata na majalisar Dattawa wanda ke dauke da sa hannun Misis Folashade Bello a madadin Shugaban hukumar, Lawal Daura wanda a cikin rahoton aka nuna cewa Magu bai cancanci shugabantar EFCC saboda yana da laifin rashawa.
Daga baya kuma majalisar ta samu wani sabon rahoto daga hukumar ta DSS ta hannun Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Majalisa, Ita Enag wanda a cikin rahoton aka nuna cewa Ibrahim Magu ya cancanci rike hukumar ta EFCC, lamarin da ya janyo rudani a tsakanin ‘yan majalisar a kan ko wane rahoton ne sahihi.