Wani Sabon Fada Ta Barke Tsakanin Yan Tawaye Da Sojojin Sudan Ta Kudu


4bk78db90ec5729zgg_800c450

 

Gwamnatin kasar Sudan ta Kusu Ta Bada Labarin Cewa an kashe mutane 15 a fadan da ta barke tsakanin sojojinta da na yantawaye karkashin Riech Marchar

Kamfanin dillamcin  labarun reuters ya khabarta cewa sabon fadan ya barke ne a jihar Unity na tsakiyar kasar sannan an kashe mutum kimani 15 da kuma raunata wasu da dama adag bangarorin biyu. Shugaban yan tawayen Riek Marcha ya birnin Birnin Joba babban birnin kasar ne bayan wani yaki wanda dakarunsa suka yi da sojojin shugaba Silva Kirr a tsakanin ranakun 9-11 na watan Yulin da ya gabata.

Sannan bayan warkewa daga raunuka da ya samu a lokacin ya sha alwashin daukar fansa da kuma kawo karshen gwamnatin Silvakirr wacce ya kira ba ta democradia ba.

Tun watan Decemban shekara ta 2014 ne bangarorin biyu masu wakltan manya manyan kabilun kasar suka fafatawa kan shugabancin kasar mai arzikin man Fetur,. Dubban mutane fararen hula ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka zama yan gudun hijira tun lokacinda yaki ya barke tsakanin bangarorin biyu.

You may also like