Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta sanar da kama wani saurayi mai shekaru 18 bisa zargin yi wa wata karamar kanwarsa mai shekaru 8 fyade.
An gurfanar da saurayin da ake zargi mai suna Sa’idu Abdullahi a gaban kotun majistire ta Katsina inda ake tuhumar sa da laifin fasikanci da wacce ba ta halatta masa ba, wanda ya sabawa kundin dokoki na Penal Code sashi na 390.
A jawabin farko na gabatar da kara ‘yan sandan sun shaidawa kotun cewa, wanda ake kara Sa’idu, wanda kuma ke karatu a matakin karamar sakandire, dan uwa ne na jini ga ita yarinyar da ya yi wa fyade. Suna zaune ne tare da iyayen su a unguwar Jan Bango dake cikin garin Katsina.
Ana zargin cewa saurayin ya yaudari yarinyar ne zuwa bandakin da ma’aikatan kamfanin mulmula karafa na Katsina, wanda ke makwaftaka da gidansu, ke amfani da shi, inda ya nuna mata karfi ya yi lalata da ita.
Daga nan ne aka dauki yarinyar zuwa babban asibitin Katsina, don a binciki lafiyar ta.
Bayan an gurfanar da shi gaban alkali, dan sandan da ya gabatar da karar Sani Ado ya bukaci a kara bashi lokaci don ya kara zurfafa bincike.
Alkalin Majistire, mai Shari’a Fadila Dikko ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu, 2018 then adjourned the matter to February 14, 2018 don cigaba da sauraron karar, yayin da aka ba da wanda ake zargi beli, kafin a koma kotun.