Wani Saurayi Ya Yi Yunkurin Kashe Budurwarsa Saboda Zata Auri Wani A Katsina



Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani mai suna Abubakar Musa, dan shekaru ashirin da uku da haihuwa dake karamar hukuma Charanchi bisa zargin yunkurin hallaka budurwarsa da suka kwashe shekaru biyar suna tare. 

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, Benson D. Gwana ya ce a bincike da rundunar ta gano Abubakar ya dauki A’isha Dikko a babur ya nufi dajin Tamawa da ke karamar hukumar Kurfi, inda ya fiddo wuka ya yi mata yanka rago, wanda a zaton sa ta mutu ya baro ta cikin jini. Ashe tana da sauran kwana. Inda wasu mutane sun zo wucewa suka lura da halin da take ciki suka yi gaggawar kai ta asibitin garin Kurfi, inda yanzu haka tana samun sauki. 

An tambaye shi ko me ya sa ya aikata wannan mummunan aiki ga masoyiyar sa, ya ce saboda kaunar dake tsakanina da ita kwatsam sai na ji an ce za ta yi aure, shi ne na kudiri kashe ta har lahira. Amma dai yanzu yana da na sani aikata hakan.

You may also like