Wata jaririya yar wata shida aka rawaito cewa mahaifinta ya kashe ta a yankin Obada dake Abeokuta babban birnin jihar Ogun.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya ce yarinyar mai suna Precious Koku mahaifinta ne, Andrew Koku y ya kashe ta dagangan tunda mahaifiyarta ta fita ta barta a gida cikin koshin lafiya.
A cewar mai magana da yawun rundunar yan’sandan mahaifiyar yarinyar, Omowumi Taleda ta kai rahoto ofishin yan sanda na shiya dake Adigbe cewa “ta bar gida domin ziyarar ɗanta da suka haifa da tsohon mijinta inda tabar yarinyar yar wata shida a gida tare da mahaifinta amma kawai sai ta dawo ta iske gawar jaririyar.”
“takara da cewa jaririyar na cikin koshin lafiya kafin tabar gida amma cikin sa’a ɗaya da fitar ta jaririyar ta mutu hakan ne yasa take zargin maigidan nata tun da shine kaɗai mutumin da yakasance da jaririyar .
“Bayan da tayi korafi ne sai baturen yan sanda na Adigbe, CSP Sunday Oladipo ya tura yan sanda masu bincike zuwa wurin da abin yafaru inda aka kama mutumin da ake zargi a ranar 24 ga watan Disamba.”
Da akayi masa tambayoyi Oyeyemi ya bayyana cewa “mutumin da ake zargi ya amince da aikata laifin kuma yayin hakan ne saboda yana fargabar matar tasa tana son komawa gidan tsohon mijinta kuma idan ta koma ba zai iya kula da yarinyar ba dalilin da yasa ya kashe ta kenan.”