Wani wakili a majalisar wakilai ta tarayya ya sauya sheka daga jam’iyar Labour zuwa APC


Ogunwuyi Segun, dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Oyo a ƙarƙashin jam’iyar Labour ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.

Yusuf Lasun, mataimakin shugaban majalisar shine ya sanar da batun sauya sheƙar ya yin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Segun dake wakiltar mazabar Ogomosho ta Kudu/arewa da kuma Orie ya ce yabar jam’iyar ta Labour ne saboda rabuwar kai da aka samu cikin jam’iyar.

Sauya sheƙa ta ƙarshe da aka samu majalisar ita ce ranar 23 ga watan Janairu lokacin da wakili Mayowa Akinfolarin, ya sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.

Kusan wakilai tara ne suka sauya sheƙa daga jam’iyu da dama a majalisar cikin shekara daya data wuce.

You may also like