Wani ya sanyawa karensa suna BUHARI. 


 

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta chafke wani mutum wanda ya sanya wa karensa suna ”Buhari”.
An dai ce mutumin mai suna Joe Chinakwe ya rubuta sunan ‘Buhari’ a jikin karen abin da ke nufin sunan da ya sanya masa ke nan.

Bayanai sun nuna cewa Joe yana da makwabci mai suna Buhari wanda kuma ba sa ga maciji da juna.Kuma makwabcin nasa ne ya kai karar sa ga rundunar ‘yan sandan jihar, a inda ‘yan sandan suka cafke Joe.

Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar ta ‘yan sandan ta jihar Ogun, ya ce sun kama Joe Chinakwe, bisa zargin sa da yin ɓatanci ga sunan makwabcinsa da kuma neman tada zaune tsaye.

A wasu kasashe dai kamar Turai kare wata dabbace mai matukar daraja da mutane suke girmamawa, har ma suke raɗa masa sunan da ya burge su.

Sai dai kuma a wasu yankunan kamar Afirka, ba a dauki kare da wata daraja ba kuma ana daukar sanyawa karen sunan mutum tamkar cin zarafi ne ga mai sunan.

You may also like