Wanne irin wa’azi limamin coci mai sa azumin mutuwa ke yi wa mabiyansa?Kenyan Pastor

Asalin hoton, YOUTUBE

Bayanan hoto,

Fasto Mackenzie sau da yawa na yin wa’azi cikin ƙaraji ga ɗumbin mabiya

Shugaban ƙungiyar Kirista mai ayyuka irin na asiri a Kenya zai bayyana a gaban kotu cikin makon gobe, yayin da ake ci gaba da aikin tono kaburburan haɗaka da aka binne matattu. Aƙalla gawa 90 aka gano zuwa yanzu.

An ba da rahoton cewa Fasto Paul Nthenge Mackenzie ya rufe cocinsa mai suna Good News International Church, shekara huɗu da ta wuce bayan ta shafe kusan shekara ashirin tana aiki.

Sai dai BBC ta bankaɗo ɗaruruwan wa’azozinsa da har yanzu suna nan, ana samun su a intanet, wasu ma ga alama an naɗe su bayan wancan lokaci.

Shin wanne labari suke bayarwa game da mutumin da ke sanya mabiyansa su zauna da yunwa har su mutu?Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like