
Asalin hoton, Super Eagles
Super Eagles za ta buga wasa na hudu a rukunin farko a gidan Guinea Bissau ranar Litinin, domin neman shiga gasar kofin Afirka.
Wasa na biyu kenan da Super Eagles za ta kara da Guinea Bissau, wadda ta doke ta 1-0 ranar Juma’a a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, Najeriya.
Daga nan Super Eales za ta buga wasa na biyar a cikin rukuni ranar Litinin 12 ga watan Yuni, inda za ta karbi bakuncin Saliyo.
Ranar Litinin 4 ga watan Satumba, Najeriya za ta karbi bakuncin Sao Tome a wasa na shida na karshe a rukunin farko.
Guinea Bissau ita ce ta daya a rukunin farko da maki bakwai, bayan da ta ci Super Eagles da Sao Tome da yin canjaras da Saliyo.
Super Eagles ta koma ta biyu da maki shida, bayan nasara a kan Saliyo da Sao Tome.
Sao Tome za ta karbi bakuncin Saliyo ranar Lahadi 26 ga watan Maris.