MANCHESTER UNITED Ta samu nasara a wasan ta na farko na firimiya na England da ci Uku da daya. Kungiyar ta Manchester United tayi tattaki ne har zuwa gidan takwarta ta AFC Bounemouth a inda ta samu nasara a wasan.
Dan wasan Kungiyar Juan Mata shiya fara zura Kwallo a minti 40 da fara wasan, inda daga bisani Waynee Rooney da Sabon dan Wasan da Kungiyar ta siya wato Ibrahimovic suka ci kwallaye guda biyu.