Wasanni: Manchester United Ce Kungiyar Da Tafi Kowacce Kungiya Arziki



Manchester United ita ce kungiyar kwallon kafa mafi arziki a illahirin Turai, inda darajarta ta kai kimanin fam biliyan 2.6 a cewar wata cibiyar harkokin kasuwanci KPMG.

Zakarun gasar Europa League din sun shiga sahun gaba na kididdigar cibiyar inda ta sha gaban gaggan ƙungiyoyin Spaniya, Real Madrid da Barcelona.

Nazarin ya bibiyi hakkokin yada wasannin kungiya, da yiwuwar kawo ribarta da shahara da damammakin buga wasanni da mallakar filin wasa.

Nazarin wanda ya kunshi kungiya 32, kulob-kulob din Ingila sun yi mamaya, inda suka kankane matsayi shida a cikin gurbi guda goma na sama.

Shugaban harkokin wasanni a cibiyar KPMG kuma mawallafin rahoton, Andrea Sartori ya ce daukacin darajar harkar wasannin kwallon kafa ta bunkasa a shekarar da ta gabata.

A cewarsa: “A lokaci guda wannan ya bayyana wani bangare na bunkasar yada wasannin kwallon kafa da fadada harkokin kasuwancin kulob-kulob a fadin duniya, da jarin da suke zubawa don mallakar kadarori na kashin kai, da na zamani, bugu da kari kuma tsare-tsaren gudanarwa masu dorewa na daga cikin manyan dalilan da suka janyo wannan bunkasa.”

“Ta fuskar darajar hakkin yada harkokin wasanni, Gasar Firimiyar Ingila ta yi wa sauran takwarorinta na Turai zarra, ko da yake su ma sauran manyan gasannin kasashe sun fito da kayyatattun tsare-tsare don yin gogayya wajen samun magoya baya a fadin duniya.”
Manyan kungiyoyin Turai guda 10 ta fuskar ‘darajar harkokin cinikayya’
1:- Manchester United -3.09bn euros
2:- Real Madrid – 2.97bn euros
3:- Barcelona – 2.76bn euros
4:- Bayern Munich – 2.44bn euros
5:- Manchester City – 1.97bn euros
6:- Arsenal – 1.95bn euros
7:- Chelsea – 1.59bn euros
8:- Liverpool – 1.33bn euros
9:- Juventus – 1.21bn euros
10:- Tottenham – 1.01bn euros

Sai dai Mista Sartori ya ce kungiyoyin sun gaza yin tasiri a daidaikunsu wajen bunkasa kudin shiga ta fuskar yada wasanni.

A bana, darajar kungiyoyin Turai 10 ta karu da fiye da yuro biliyan daya, ninki biyu idan an kwatanta da shekarar 2016.

Tottenham Hotspur da Juventus ta Italiya ne sabbin shiga rukunin hamshakan kungiyoyin Turai, inda Tottenham ta jeho Paris Saint-Germain ta Faransa daga matsayi na goma.

Duk da mamayar da kungiyoyin Firimiya suka yi, Spaniya ce kasa guda daya da ke da kungiya biyu da rahotanni suka ce na da “darajar harkokin kasuwanci” ta fiye da yuro biliyan biyu, Real Madrid da Barcelona.

You may also like