Wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 7 a wani ƙauye dake Kaduna


Mutane da ba su gaza 7 ne aka kashe a wani hari da wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne suka kai kan ƙauyen Kaguru dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Wasu mazauna ƙauyen da dama sun samu raunuka ya yin da wasun su  suka tsere zuwa daji.

A cewar wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa, harin ya faru ne ranar Laraba da misalin karfe 7 na dare.

Ya ce Fulani masu yawa ne ɗauke da makamai suka buɗe wuta akan ƙauyen tare da ƙona gidajen su.

“Wajen karfe 7 su ka zo, suna zuwa suka fara harbi tare da cinnawa gidaje wuta.Gidaje da yawa aka cinnawa wutar.

“Mutane 7 aka kashe nan take mun binne matattun a daren jiya, mutane da yawa sun tsere cikin daji domin tsira da rayukansu muna zaune cikin fargaba muna kira ga gwamnati kan ta bamu jami’an tsaro,” ya ce

Sai dai har ya zuwa yanzu babu wata sanarwa daga rundunar yan sandan jihar dake gasgata kai harin.

You may also like