Wasu ƴan Najeriya dake Libya basu son dawowa gida


Hoton wasu yan Najeriya da suka dawo daga kasar Libya

Jami’in difilomasiya dake kula da ofishin jakadancin Najeriya a ƙasar Libya Mista Iliya Fashano yace wasu daga cikin yan Najeriya dake Libya sun ki yarda a dawo dasu gida duk da yanayi marar da daɗi da suke ciki.

Fachano ya fadawa kamfanin dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa:”Ba dukkanin su bane suke son komawa gida ba.”

“Kafin ka taimaka musu dole ne su saka haka hannu a fom na  amincewa bayan haka sai abarsu takardar izinin tafiye-tafiye ta gaggawa.

“Ina son jama’a su san cewa akwai yan Najeriya da basa son su dawo gida duk da yanayi mai muni da suke ciki kuma maganar gaskiya babu ta yadda za  a yi ka sako su a jirgi ba tare da amincewarsu ba.”

You may also like