Wasu Alkalan Kotun Koli Sun Ajiye Mukamansu. 


Wasu Alkalan kotun koli biyu, Inyang Okoro da Sylvester Ngwuta wadanda ke cikin Alkalai bakwai da hukumar tsaro na farin kaya suka cafke bisa zargin rashawa sun dakatar da gudanar da duk wani aiki da ya jibinci shari’a.
Sai dai kuma hukumar da ke kula da kotuna ta kasa ta ce ba za ta sallami Alkalan da ake zargi da laifin rashawa ba kasancewa ana ci gaba da matsim lamba kan hukumar kan ta Ladaftar da wadannan Alkalan.

You may also like