Wasu Bama- Bamai Sun Fashe A Garin MaiduguriRahotanni daga garin Maiduguri babban birnin jihar Borno sun nuna cewa an samu tashin tagwayen bama-bamai a cikin dandazon jama’a a babban kasuwar yankin.
Bama-baman sun tashi ne da misalin karfe 8:48 na safiyar yau.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Victor Isuku ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ya ce lamarin ha auku ne a kusa da tsohon ofishin NEPA wanda ba shi da nisa da Monday Market.
Saidai har zuwa yanzu babu cikakken rahoton barnar da tashin bama-baman suka yi.
Wurin da bama-baman suka tashi yana daya daga cikin wuraren da ke tara jama’a a Maiduguri kasancewar ana harkokin kasuwanci inda mutane daga ciki da wajen garin suke shigowa.
Duk da cewa babu tabbacin yadda aka tada bama-baman amma wata majiya ta rawaito cewa ‘yan kunan bakin wake ne suka tayar.

You may also like